Babban Bankin Najeriya Ya Bukaci ‘Yan Nijeriya Su Rika Sarrafa Sabbin Kudi Na Naira
Aliyu Bello Mohammed, Katsina
Babban Bankin Najeriya ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su rika kula da sabbin takardun kudin Naira a hankali yayin da ake amfani da su a fadin kasar.
Bankin Apex ya yi wannan roko ne a wani sakon bidiyo da ya wallafa a shafin Twitter.
Babban bankin ya bukaci ‘yan Najeriya da su rungumi sabbin takardun kudi na Naira, saboda an inganta matakan tsaro domin dakile ayyukan jabu.
A baya dai CBN din ya sanar da cewa, za a sake fasalin takardun kudi na Naira 200, 500, da 1000 kuma za a daina amfani da tsofaffin takardun kudi a ranar 31 ga Janairu, 2023.
Leave a Reply