Gwamnan jihar Ebonyi a kudu maso gabashin Najeriya, Engr. David Umahi ya jajantawa iyalan Obiozor, al’ummar jihar Imo, al’ummar Igbo da Najeriya baki daya bisa rasuwar shugaban kungiyar Ohaneze Ndi-Igbo, Farfesa George Obiozor.
Ya ce mutuwar Obiozor ta same shi da kaduwa da mamaki, yace wannan wani babban rashi ne ga kasa.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman ga gwamna kan harkokin yada labarai da dabaru Mista Chooks Oko ya fitar a Abakaliki babban birnin jihar.
Umahi ya jaddada cewa, rasuwan dattijon ta haifar da wani babban gibi da ke da wahalar cika ga al’amuran yankin Kudu maso Gabas musamman ma Najeriya baki daya.
“Na samu labarin rasuwar shugaban Ohaneze Ndigbo, Farfesa George Obiozor a matsayin babban rashi”
Karanta Hakanan: Gwamnan Anambra Ya Yi Makokin Ohaneze Ndigbo
“Da ban yarda da labarin ba, sai da dan uwana kuma gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma ya tabbatar mani da hakan.”
“Mutuwar Obiozor ta haifar da babban rashi, ba a kasar Igbo kadai ba, har ma a fadin kasar baki daya”
“Ya kasance mai karfin fada a ji wajen samar da zaman lafiya a kasar nan ta hanyar dagewar da yake yi na tabbatar da daidaito, adalci da gaskiya a dukkan bangarori. Ya kasance mai karfin fada a ji a siyasar duniya kuma ya yi wa Najeriya hidima mai inganci a matsayin jakada da Darakta Janar na Cibiyar Kula da Harkokin Kasa da Kasa.”
“Abin bakin ciki ne cewa dole ne ya tafi lokacin da muke Bukatar shawarar shi.” Ummahi tace.
Gwamnan ya bukaci ‘yan uwa da daukacin al’ummar Igbo da ‘yan Najeriya baki daya da su jajanta akan wannan rashin da akayi, domin Allah ne yake da ikon sanin makomar kowane mutum.
Leave a Reply