Take a fresh look at your lifestyle.

Gidan Yari: An kasha fursunoni 14 ,24 Sun Tsere A Arewacin Mexico

Aiasha Yahaya,Lagos

0 204

A arewacin Mexico bayan da wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan kungiyar masu safarar miyagun kwayoyi ne, sun bude wuta a gidan yarin jihar Chihuahua jim kadan bayan karfe 7:00 na safe (14:00 agogon GMT), fursunoni 24 ne suka tsere yayin da aka kashe masu gadin gidan yarin 10, tare da fursunoni 4, a lokacin, mummunan harin da aka kai a birnin Ciudad Juarez da ke kan iyaka.

 

 

 

Hukumomi sun tabbatar da cewa ‘yan bindigar sun isa wurin ne a cikin motoci masu sulke inda suka fara harbin masu gadi. Har ila yau, fadan da aka yi a gidan yarin, inda fursunoni daga kungiyoyin masu aikata laifuka daban-daban, da masu safarar miyagun kwayoyi ke zama, ya kai ga jikkatar mutane kusan 13 Inda hudu daga cikinsu suna jinya a asibiti.

 

 

 

A waje ‘yan uwa suka taru suna rungumar juna suna kuka suna jiran labari. Wata mata ta ce maharan suna sanye da bakaken kaya ne, sun fi ‘yan sanda makamai, kuma suna harbin duk wata mota da ta wuce. An kira sojoji da jami’an tsaron kasar da su marawa hukumomin yankin baya.

 

 

 

 

An kira sojoji da jami’an tsaron kasar da su marawa hukumomin yankin baya. A halin da ake ciki kuma, kafin guduwar, wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun yi wa ‘yan sanda wuta a kan titin da ke kusa da wurin, inda suka tayar da wata mota ta bi ta inda aka kama wasu mutane hudu.

 

 

 

Garin dai ya sha fama da tashe-tashen hankula na tsawon shekaru tsakanin ‘yan adawar Sinaloa da masu safarar miyagun kwayoyi na Juarez, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane a cikin shekaru goma da suka gabata.

 

 

Gidan yarin kuma ya kasance wurin da aka yi bore a cikin watan Agustan da ya gabata inda wata tarzoma a cikin gidan yarin ta fantsama kan tituna, inda mutane 11 suka mutu.

 

 

 

Dukkan abubuwan biyun sun jadada irin karfin da har yanzu masu fafutuka ke yi a tsarin gidan yari. Masu gabatar da kara a birnin, wanda ke kan iyaka daga El Paso, Texas, sun yi alkawarin gudanar da bincike kan sabon harin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *