Kocin Al Nassr Rudi Garcia ya ce sayen Cristiano Ronaldo babban ci gaba ne ga kwallon kafar Saudiyya bayan da dan wasan Portugal din ya isa Riyadh gabanin kaddamar da shi a hukumance ranar Talata.
Ronaldo, wanda kwantiraginsa ya kare bayan rabuwarsa da Manchester United a watan Nuwamba, ya koma Al Nassr a makon da ya gabata kan yarjejeniyar shekara biyu da rabi da kafafen yada labarai suka kiyasta ta kai sama da Yuro miliyan 200 ($213.30).
Garcia, wanda ya jagoranci Lille, AS Roma, Olympique Marseille da Olympique Lyonnais ya ce: “Sanya dan wasa girman Cristiano Ronaldo abu ne na ban mamaki kuma yana ba da gudummawa ga ci gaban kwallon kafa na Saudiyya.”
“Mun yi farin ciki da zuwansa. Manufar farko ita ce yin aiki don ya dace da ƙungiyarmu, don jin daɗin buga wa Al Nassr wasa, da kuma nishadantar da magoya baya. “
Za a bayyana Ronaldo a gidan Al Nassr Mrsool Park, inda ake sa ran magoya bayansa 25,000 za su hallara.
Leave a Reply