Take a fresh look at your lifestyle.

Theresa Peter

0 112

Novak Djokovic baa i samu halartar budewasan Indian Wells da Miami ATP 1000 a wannan shekara idan har ba a yi masa allurar rigakafin Covid-19 ba, bayan da hukumomin Amurka suka ce wadanda ba ‘yan asalin kasar ba suna bukatar riga kafi kafin su shiga kasar.

 

Sanarwar da Hukumar Kula da Sufuri ta fitar a ranar Laraba ta ce, an bukatar matafiya da jiragen sama na kasashen waje su yi cikakken rigakafin cutar har zuwa ranar 10 ga Afrilu.

 

Za’a gudanar da was an Indian Wells daga watan Maris 6-19 da Miami Open daga Maris 20 zuwa Afrilu 2 kuma Djokovic na fuskantar hadarin rasa mahimman gasa guda biyu idan bai yi allurer riga kafi ba.

 

Dan kasar Sabiya, mai shekaru 35, ya kasa kare kambun wasan Tenis cin kofin Australian Open a bara, bayan da aka kore shi daga kasar a jajibirin babbar wasa.

 

Djokovic, wanda ya lashe kambun Grand Slam 21, shi ma bai samu damar zuwa New York ba don gasar was an Tenis na US Open a 2022 ba tare da shaidar riga-kafi ba, dalili daya tilasta masa asara gasa a Indian Wells da Miami.

 

Zakaran Australian Open sau tara a halin yanzu yana atisayen fuskantar was an Tenis a kakar 2023 a Adelaide don gasar da a’a gudana na Australian Open daga ranar 16 zuwa 29 ga watan Janairu, bayan dakatar da shi na tsawon shekaru uku a kasar a watan Nuwamba.

 

Wannan shawarar ta buɗe masa hanyar nuna kwarewa karo na 10 a Grand Slam kuma yana da alamar samun Nasra akan Rafa Nadal.

 

 

 

Djokovic, wanda a baya ya bayyana cewa zai yi kewar Grand Slams lokacin da yake shan maganin Covid, ya ce a makon da ya gabata ba zai taba mantawa da yadda aka kore shi daga Ostireliya ba amma yana fatan ci gaba da wasan.

 

“Abin da ya faru watanni 12 da suka wuce bai kasance mai sauƙi ba na ɗan lokaci amma a lokaci guda, dole ne in ci gaba,” in ji Djokovic a makon da ya gabata a taron manema labarai na farko tun lokacin da ya sauka a Australia.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *