Take a fresh look at your lifestyle.

Babu Abin Da Zai Dakatar da Zaben 2023-FG

0 167

Gwamnatin Tarayya ta dage, cewa babu wata baraza daga kowane bangare da za ta iya hana gudanar da zaben 2023, wanda ya rage saura wata guda.

 

 

Ministan yada labarai Alhaji Lai Mohammed ya bayyana matsayin gwamnati a lokacin da yake mayar da martani ga ikirarin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta yi na cewa ba za a iya gudanar da zabukan a wasu jihohin ba saboda barazanar tsaro.

 

 

Yayin da yake magana da manema labarai a Abuja ranar Talata, ministan yada labaran ya bayyana cewa ”ba wata barazana da za ta iya hana zaben kamar yadda aka tsara.”

 

 

“Matsayin Gwamnatin Tarayya shine za a gudanar da zaben 2023 kamar yadda aka tsara. Babu wani abu da ya faru da ya canza wannan matsayi.

 

“Muna sane da cewa INEC na hada kai da jami’an tsaro domin ganin an gudanar da zaben cikin nasara a fadin kasar nan.

 

 

“Hukumomin tsaro sun kuma ci gaba da tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa suna bakin kokarin su wajen ganin an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali. Don haka, babu wani abin fargaba,” inji Mohammed.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *