A ranar Akhamis Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya Ziyarci Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Emefiele, wanda ya dade yana hutu ya kai iyara a fadar Shugaban kasa karo na farko a wannan Shekara.
Gwamnan Babbabn Bankin ya isa Fadar Shugaban Kasa da misalin karfe 14: 30 GMT, yayi wata ganawa ta sirri na tsawon mintuna 25,tare da Shugana Najeriya.
Da manema labarai suka nemi jin ta bakin shi game da Ziyarar da kuma ganawar shi da Shugaba Buhari,bai amsa tambayar su ba.
Labarin Emefiele ya ki amsa gayyatar ‘yan Majalisar Dokokin kasa na wani rahoton kama shi ,wanda daga baya hukumar tsaro ta farin kaya ta musanta.
Leave a Reply