Take a fresh look at your lifestyle.

Ma’aikatan Sufuri a Senegal na yajin aiki saboda matakan kiyaye hanya

0 13

Bangaren sufuri a kasar Senegal ya shiga yajin aikin, inda kungiyoyin kwadago da dama suka hada karfi da karfe domin yin tir da matakan da aka dauka na yaki da matsalar rashin tsaro.

 

An sanar da wani shiri bayan wani mummunan hatsarin da ya faru a sashen Kaffrine.

 

Amma wasu masu jigilar kayayyaki sun nuna rashin amincewarsu da rashin tuntubar juna, da kuma rashin yiwuwar aiwatar da wasu matakan.

 

A ranar litinin din da ta gabata, hatsarin motar bas ya yi sanadin mutuwar akalla mutane 19, wanda ya kawo adadin mutanen da suka mutu a hadarurrukan mota zuwa kusan 60 a cikin kwanaki kadan.

 

Gwamnati ta mayar da martani ta hanyar sanar da matakan kusan dozin biyu, da suka hada da kayyade bas da manyan motoci zuwa kilomita 90 a cikin sa’a guda (mph 56), da hana motocin safa da daddare da kuma haramta shigo da tayoyin da aka yi amfani da su, wadanda ake zargi da haddasa hatsarin makon jiya.

 

Duk da haka, wasu ƙungiyoyin sufuri sun kira wasu abubuwan da ba su dace da gaskiya da salon rayuwa ba.

 

A cewar bankin duniya, kasar Senegal, mai mutane miliyan 17, tana samun asarar rayuka 24 a kan kowane mutum 100,000 a kowace shekara.

Leave A Reply

Your email address will not be published.