Gwamnatin Jihar Ebonyi ta bakin ma’aikatar tsaron cikin gida ta bayyana shirinta na dakile duk wani nau’i na miyagun laifuka a jihar.
Kwamishinan tsaro na cikin gida na jihar, Prince Etta Uka ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa dake tsohon gidan gwamnati Abakaliki, babban birnin jihar.
Uka ya ce ma’aikatarsa ta yi nasara kan harkar dakile miyagun laifuka a jihar ba don wani abu ba sai don ma’aikatar ta na aiki tare da sauran hukumomin tsaro na jihar.
Ya bayyana cewa “A daya bangaren kuma don tabbatar da cewa babu laifi a cikin jihar, muna aiki tare da hadin gwiwar hukumomin tsaro na yau da kullun kamar ‘yan sandan Najeriya da Tsaron Najeriya da Civil Defence da hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa da dai sauransu, idan muka kama duk wanda ya barnatar da kayayyakin aiki, sai mu mika shi ga jami’an tsaro da na Civil Defence, idan matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi ne, sai mu mika wanda ya aikata laifin ga hukumomin shaye-shayen miyagun kwayoyi, idan kuma ya zama wani abu da ya shafi ’yan sanda, don haka mu mika shi ga hukumomin da laifi.”
Ya yabawa ma’aikata a ma’aikatar da suke yin abubuwan al’ajabi wajen tabbatar da cewa jihar ba ta da laifi.
“Kwanaki kadan da suka wuce, wani ya sayi bindigu kirar AK-47 da harsasai na rai guda 5 wanda ya yi nasarar zuwa jihar Ebonyi amma zuwa wurin jami’an tsaron cikin gida sun kama shi suka kwato makaman yaki tare da mikawa ‘yan sanda.”
Ya yabawa Gwamnan Jihar, Francis Nwifuru bisa yadda a kodayaushe ke ba da dukkan kayan aikin da ma’aikatar ke bukata don gudanar da ayyukansu.