Fadar Shugaban kasa ta ce rahoton da aka yi ta yadawa na jifan shugaba Muhammadu Buhari da aka yi a Kano abin dariya ne kuma ba gaskiya ba ne.
Kakakin Shugaban Kasa, Garba Shehu, yayin da yake mayar da martani ga rahoton, ta wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce:
“Mun ga rahotannin karya na jifa da duwatsu da suka faru a unguwar Hotoro a Kano a ranar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyara birnin a ranar Litinin, lamarin da ko da karami ne, ya kamata kowa wani mai kishin kasa ya yi Allah wadai da shi.
“Gaskiyar abin dake faruwa kamar yadda jami’an tsaro suka yi bayani a kan rikicin da ya barke tsakanin hukumar sufurin mota ta Kano, KAROTA da ‘yan baranda da wasu da ba a san ko su wanene ba suka dauki hayarsu a lokacin da shugaban ke zuwa wata liyafa a gidan gwamnati, bayan ya gama kaddamar da ayyukansa.
Shugaban ya je jihar ne domin gudanar da ayyukan ci gaba da tsaron rayuwar talakawa kuma abin farin ciki shi ne yadda al’ummar jihar Kano suka yi masa godiya bisa ci gaban jihar da kasa baki daya a karkashin gwamnatinsa.”
Shehu ya ce shugaban kasar da magoya bayansa suna da cikakkiyar masaniya kan makircin ‘yan adawa, wadanda suke ganin za su iya kawar da hankalin shugaban kasar.
Ya ce shugaban ya mayar da hankali sosai wajen samar da ribar dimokuradiyya ga ‘yan Najeriya.
Leave a Reply