Hukumar kula da kwallon kafa ta Afrika ta fitar da jerin sunayen filayen wasa da aka amince da su don buga wasannin neman tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka na 2023.
KU KARANTA KUMA: An Shirya Wasan Karshe Domin Gasar Cin Kofin Kasashen Afirka na 2023
Filaye biyu ne kawai aka amince da su a Najeriya kuma su ne filin wasa na MKO Abiola, da ke Abuja da kuma filin wasa na Goodswil Akpabio da ke Uyo.
Daga cikin kasashe 48 da za su fafata, 24 ba su da filayen wasa da aka amince da su, wanda hakan ke nufin za su buga wasanninsu na gida a fili.
Kasar Masar ce ta fi kowacce yawan filayen wasa 6 da aka amince da ita, sai Aljeriya da Maroko wadanda ke da filayen wasa 5 da aka amince da su kowanne.
Za a ci gaba da wasannin share fage a watan Maris na 2023 kuma Super Eagles ta Najeriya ita ce kan gaba a saman rukunin B da maki 6 a wasanni biyu.
Leave a Reply