Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF da hukumar kula da ruwa da tsaftar mahalli ta jihar (WASH) sun fara tantance irin barnar da aka yi gabanin gyarawa da maye gurbin ababen more rayuwa da suka lalace a wasu sassan jihar Anambra da ambaliyar ruwa ta bara.
Muryar Najeriya, ta ruwaito cewa UNICEF ta fara tantancewar ne a makon da ya gabata kuma za ta fara gyara kayayyaki a makarantun gwamnati da kasuwanni da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko da sauran wuraren taron jama’a nan ba da jimawa ba.
Ka hana fitowar bayan gida daya daga cikin dalilan gyare-gyaren, VON ta kara gano shi ne na hana yin bahaya a fili dake haddasa cutar kwalara a yankunan da lamarin ya shafa. Binciken da gyare-gyaren ya kai jami’an zuwa kananan hukumomin Anambara ta Gabas da Anambara ta Yamma da Ayamelum da Awka ta Arewa da kuma Ogbaru inda ambaliyar ta lalata mafi yawan kayayyakin jama’a, yayin da a Ekwusigo da lhiala lareas, tawagar UNICEF ta gano cewa gonaki da dama da wasu gine-gine ta lalace.
Jimillar cibiyoyi 83 a cikin kananan hukumomi bakwai ne ambaliyar ta shafa, daya daga cikin abokan aikin na UNICEF, Mista Mike Onyemelukwe ya yabawa kungiyar ta duniya da kuma gwamnatin jihar Anambara bisa kokarin da suke yi na inganta rayuwar wadanda abin ya shafa, inda ya bayyana cewa hakan zai taimaka matuka wajen rage bahaya a fili, wanda ya zama ruwan dare a yankunan al’ummomin sakamakon ambaliyar ruwa.
A cewar shi, za a iya hana yin bayan gida a fili da kwalara idan an samar da kayayyakin da ake bukata. Ya ce hukumomin bayar da agaji na da sha’awar batutuwan da suka shafi mata da yara.
Manajan shirye-shirye na hukumar samar da ruwan sha da tsaftar muhalli ta jihar (RUWASSA) Mista Tochukwu Nwosu ya yi kira ga gwamnatin jihar Anambara da ta ci gaba da tallafa wa UNICEF a kokarinta na samar da ruwan sha da tsaftar muhalli ga al’ummomin da ba su amfana da shirin na UNICEF, cewa wasu al’ummomin da ambaliyar ruwan ba ta shafa su ma ba su da abubuwan more rayuwa
Leave a Reply