Take a fresh look at your lifestyle.

UN ZATA KWASHE KARIN FARAR HULA A MARIUPOL

0 203

Majalisar Dunkin duniya UN ta sanar da cewa yau Juma’ a zata fara kwashe kimanin farar hula 200 da suka makale a masanaantar sarrafa karafa dake Mariuopol sakamakon fada da ake gwabzawa.

Sakatare Janar na UN , Antonio Guterres ya sanar da haka cewa, Za’ ayi duk abunda ya dace na kwashe farar hula daga yankin.”

Shugaban Rasha Vladimir Putin yace a shirye rundunar sojin shi suke na kare rayukan farar hula,amma dole abokan gaba su yi saranda.

Hakazalika Shugaban Rasha y ace an samu nasarar kwace yankin Mariupol, ya umurci dakarun shi da su rufe masanaantar wadda aka gina a lokacin yakin na biyu a matsayin wajen buya.

Shugaban Ukraine  Zelensky ya jadda cewa dakarun Rasha naci gaba da luguden wuta kuma suna yunkurin kwace masanaantar.

Ka lura da irin wannan masifarl. Kuma akwai yara kanan a yayin luguden wutar na tsawon watanni,kuma ana kasha mutane makwabtan masanaantar,” a cewar shi.

 

LADAN NASIDI

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *