Take a fresh look at your lifestyle.

Hukumar Bunkasa yankin Arewa maso gabashn Najeriya NEDC zata gyara Asibitoci

TIJJANI USMAN BELLO, MAIDUGURI.

0 149

Babban Manajan Hukumar NEDC, Alhaji Muhammad Goni Alkali, ya fada hakan ga manema Labarai jim kadan bayan ya kammala zagaya Asibitocin dake garin Maiduguri.

 

 

Bubban Manajan Hukumar ta NEDC, Alhaji Muhammad Goni Alkali, ya kara da cewar “Bisa la’akari da kasancewar Asibitocin Ciwon Ido da na Hakora, tun da aka ginasu shekaru 40 da suka gabata ba’a taba gyara su ba, gashi kuma alummomin Kasashen makwabta na Jamhuriyar Niger, Camarou da Chadi, na amfana dasu baya ga alummomin wannan yankin Arewa maso gabashn Najeriya.”

 

 

Ya ce “Da haka muke ganin cewar bai kamata a zauna ana ganin wadannan asibitocin biyu na ci gaba da lalacewa ganin hakkin wannan Hukumar ta NEDC ke gyara da gina duk wasu ababe wanda alummomin wannan yankin zasu amfana, ko ta wace fuska, kama tun daga bangarorin Ilimi, kiwon Lafiya, aikin Noma, Muhalli, samarwa da Matasa aikinyi da dai sauransu.

 

 

” Wannan gyaran da Hukumarmu za ta yi wa wadannan asibitocin biyu, zai fara ne tun daga sauya fasalinsu ta yadda zai dace da na zamani, da samar da naurar kwanfutar zamani masu aiki da Kwakwalwa, da gina gidajen Ma’aikata, da gina cibiyoyin bincike da nazari, da koyarwa don amfanin Ma’aikata, Malamai da su kansu Daliban wannan yankin dama Kasashe makwabta.”

 

 

Goni Alkali, ya kara da cewar“Duk da cewar bamu kai ga kiyasta yawan kudaden da zamu kashe akan wadannan ayyukanba, to amma dai na fahimci cewar za’a gudanar da manya-manya da muhimman ayyuka a wadannan asibitocin biyu don farfado da daraja da martabansu a wannan yanki dama Kasashen makwabta, na Jamhuriyar Niger, Camarou da Chadi.”

 

 

Da yake mayar da martani a madadin gwamnatin jihar Borno, Kwamishinan kiwon lafiyan jihar, Farfesa Muhammad Arabi Alhaji, ya yaba da yunkurin aikin na Hukumar NEDC, in da ya ce

 

 

” Babu shakka babban Manajan hukumar NEDC ya cancanci yabo saboda irin wannan yunkurin gyara wadannanan Asibitocin Ciwon Ido da na Hakora saboda lalacewarsu, ganin cewar alummomin Kasashen makwabta na Jamhuriyar Niger, Camarou da Chadi, na amfana dasu saboda haka gwamnatin jihar Borno ta gode da wannan tsarin gine-ginen  Asibitocin”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *