Take a fresh look at your lifestyle.

U-23 AFCON: Najeriya za ta karbi bakuncin Guinea a Abuja

Aliyu Bello Mohammed

179

Tawagar ‘yan kasa da shekaru 23 ta Najeriya, Olympic Eagles za su karbi bakuncin takwarorinsu na Guinea a filin wasa na Moshood Abiola na kasa, Abuja a ranar Laraba, 22 ga Maris, a wasan zagaye na karshe na neman tikitin shiga gasar cin kofin Afrika na U23 na bana.

Wasan da aka shirya tun farko a filin wasa na Lekan Salami, Adamasingba, Ibadan State Oyo an koma Abuja, babban birnin Najeriya.
Domin kaiwa ga wannan matakin na gasar, zakarun na 1996 sun lallasa kungiyar ‘yan kasa da shekaru 23 ta Tanzania da ci 3-1 a jimillar wasanni a watan Oktoban 2022, inda suka yi nasara da ci 2-0 a filin wasa na Lekan Salami, Ibadan bayan da kungiyoyin biyu suka yi kunnen doki a wasan farko a Dar es Salaam da ci 1- 1.

Wanda ya samu nasara a wasa biyu tsakanin Najeriya da Guinea zai tsallake zuwa wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka na ‘yan kasa da shekaru 23 da Morocco za ta karbi bakunci a wannan shekara. Har ila yau, a gasar da ake yi a Morocco ne ‘yan wasan Afirka masu rike da tuta a gasar kwallon kafa ta maza da za a yi a birnin Paris na shekara mai zuwa.

A ranar Litinin 27 ga watan Maris ne za a fafata da Guinean a Morocco.

Comments are closed.