Hukumar kula da tashar jiragen ruwa ta Madagascar ta sanar a ranar Lahadin da ta gabata, yayin da wani jirgin ruwa dauke da su ya kife a tsibirin Mayotte na kasar Faransa, inda mutane 22 suka mutu.
Hukumar ta sanar da cewa jirgin mai dauke da mutane 47 ya kife ne a ranar Asabar a tekun Ankazomborona da ke arewacin kasar Madagascar.
Hukumar ta ce kwale-kwalen ya yi hatsari, bayan da aka ceto 23 daga cikin wadanda ke cikin jirgin, yayin da aka gano gawarwaki 22.
Sauran biyun kuma ba a ji duriyarsu ba.
Wani dan sanda da bai so a bayyana sunansa ba ya ce akasarin wadanda aka ceto sun gudu ne don gudun kada a kama su saboda yunkurin tafiya zuwa Mayotte.
Leave a Reply