Take a fresh look at your lifestyle.

INEC Ta Bayyana Makinde A Matsayin Mai Nasara A Zaben Gwamnan Oyo

0 153

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP kuma gwamnan jihar Oyo dake kudu maso yammacin Najeriya Seyi Makinde a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.

Jami’in kula da masu kada kuri’a a jihar Oyo kuma mataimakin shugaban jami’ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife a jihar Osun a kudu maso yammacin Najeriya Farfesa Adedayo Bamire ne ya bayyana hakan bayan tattara sakamako daga kananan hukumomi 33 na jihar.

Makinde ya samu kuri’u 563,756 inda ya doke abokin takararsa Teslim Folarin na jam’iyyar All Progressive Congress wanda ya samu kuri’u 256,685.

Makinde wanda ke neman sake tsayawa takara a ranar Asabar ya fafata da Sanata Teslim Folarin na jam’iyyar All Progressives Congress mai wa’adi uku da Adebayo Adelabu na jam’iyyar Accord wanda ya kasance tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *