Take a fresh look at your lifestyle.

SDP Ta Kaddamar Da Kwamitin Taro Na Kasa 2026

149

Jam’iyyar Social Democratic Party SDP a Najeriya ta ce ta sanya tsare-tsare a gaban babban taron jam’iyyar na kasa na 2026 da ke tafe tare da kaddamar da kwamitin da zai sa ido a kan lamarin.

 

Shugaban jam’iyyar na kasa Farfesa Sadiq Gombe ne ya bayyana hakan jim kadan bayan nasarar da jam’iyyar ta samu a aikin duba da tantancewa da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ke gudanarwa a Abuja babban birnin Najeriya.

 

Farfesa Gombe ya ce kwamitin zai tsara ayyukan da za su kai ga babban taron 2026 nadin takara da sauran shirye-shiryen jam’iyyar.

 

A cewarsa kwamitin na karkashin jagorancin Farfesa Usman Bugaji yayin da Mulikat Akanbi zai kasance mataimakin shugaban kwamitin taron jam’iyyar.

 

Ya kara da cewa shugaban kwamitin majalisar kan ma’adanai mai karfi Mista Jonathan Gaza Gbefwi zai yi aiki a matsayin sakatare tare da sauran shugabannin jam’iyyar da masu ruwa da tsaki.

 

Shugaban jam’iyyar SDP na kasa ya ce nan ba da jimawa ba za a aika gayyata ga masu ruwa da tsaki da ‘yan jarida don tabbatar da gaskiya da yada yadda taron ya gudana.

 

Farfesa Gombe ya lura cewa jam’iyyar ta kuma bi aikin tantancewar INEC ta hanyar gabatar da dukkan takardun da ake bukata.

 

Ya ce atisayen ya hada da tantance mambobin ta ta hanyoyi masu inganci kamar katin zabe da lasisin tuki da fasfo na kasashen waje.

 

A cewarsa, a halin yanzu jam’iyyar tana da mambobi kusan miliyan goma sha biyar masu rajista a fadin kasar nan.

 

Ya kara da cewa har yanzu ana ci gaba da rijistar ‘yan mambobi gabanin zabukan majalisun tarayya da na babban taro da kuma zabukan fidda gwani a shekarar 2026.

Comments are closed.