Hukumar Kwastam ta tara kuɗin shiga sama da naira biliyan 212 a wattani uku, ta kama tarin miyagun ƙwayoyi a Apapa
Hukumar hana fasakwaɓri ta ƙasa (kwastam) shiyar Apapa a Legas samar da kuɗin haraji naira biliyan ɗari biyu da goma sha biyu da miliyan ɗari biyar da casa’in da biyu da dubu ɗari shida da tamanin da naira ɗari bakwai da kobo casa’in da tara (N212,592,680,700.99) a cikin watan Janairu zuwa Maris na shekarar 2023.
Shugaban Kwastam na yankin Apapa, Kwanturola AB Muhammad ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar talata, ya kuma kara da cewa, rundunar ta kama wasu sunduƙai goma sha hudu da suka haɗa da haramtattun kayayyaki da ka shigo da su daga ƙasashen ƙetare irinsu man kirki, takalma, tufafin gwanjo, da itacen, da kuma miyagun ƙwayoyin tramadol, an kuma ƙiyasta kuɗinsu akan naira biliyan ashirin da biyu da miliyan casa’in da tara, dubu ɗari shida da sha takwas da naira ɗari da goma sha ɗaya.
Kwanturola AB Mohammed ya ce rundunar ta yanke shawarar aiwatar da tsare-tsaren kasafin kudi na gwamnatin tarayya da kuma wasu dokoki don tabbatar da cewa duk kayayyakin da ake shigowa ko fita da su daga tashar jiragen ruwa ta Apapa an yi nazarinsu yadda ya kamata ta hanyar ingantaccen haɗin gwiwa da musayar bayanan sirri a kan lokaci tare da yin aiki tare da sauran jami’an hukumomi na gwamnati da ke aiki a tashar jiragen ruwa ta Apapa.
Ya qara da cewa a ranar Juma’a, 31 ga Maris, 2023, jami’an hukumar sun gano wani adadi mai yawa na miyagun ƙwayoyin Tramadol mai nauyin 225mg da aka yi badda baninsu a cikin kwantena guda biyu mai tsawon ƙafa 40 masu lamba TRHU 4758549 da TRHU 6936803 inda aka gano ƙwayoyin Tramadol miliyan ɗari da arba’in da uku da dubu ɗari takwas na ƙwayar Tramadol mai nauyin 225mg wanda nauyinsu ya kai tan 10.3 (kg 10,386), ya ce an shigo da miyagun ƙwayoyin ne daga ƙasar Indiya.
“Wannan kamun guda ɗaya ƙimar kayan ya kai naira biliyan ashirin da ɗaya da naira miliyan ɗari shida Kum muna ci gaba da bin diddigin masu shigo da irin wannan kaya ba bisa ka’ida ba domin kama su, nan ba da jimawa ba za mu zaƙulo su domin fuskantar doka, domin a matsayinmu na masu hidima ga ƙasa, hakkinmu ne hana shigo da irin wannan da kaya daga ƙasashen waje domin kare lafiyar ‘yan kasa.
“Bari in yi amfani da wannan damar wajen gargadi ga masu aikata laifukan fasa-kwauri,da sub guje wa mummunan aiki da sauran laifukan da hukumar kwastam ta fitar a ƙarƙashin dokar CEMA da sauran dokoki na ƙasa, domin rundunar kwastam a Apapa kawai za ta sauƙaƙa halastatun kasuwanci ne, tare da kawar da gurɓatattun masu hada hada. In ji shi.
Da ya ke ƙarin haske ɗan gane da fitar da kayayyaki da Najeriya ta je yi zuwa ƙasashen ƙetare, kayayyakin amfanin gona irin su citta albarkatun ma’adinai da ƙarafa da dai sauransu ya ce an fitar da kayayyakin da jimillar nauyinsu ya kai ton metric ton 110,448 a rubu’in farko na shekarar 2023.
“Alkaluman da aka fitar sun nuna cewa kayayyakin da aka fitar zuwa ƙasashen waje sun kai naira biliyan saba’in da miliyan ɗari biyu da dubu ɗari takwas da ashirin da tara da naira ɗari uku da hamsin da takwas da kobo sittin da bakwai, kwatankwacin kuɗin jirgi na Free on Board (FOB) $159,845,232.84.”
Kwanturala AB Mohammed ya kuma bayyana cewa, kyakyawan sakamakon da aka samu ya faru ne duba da yadda rundunar take yin haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki da hukumomin gwamnati don tabbatar da ɗorewar ayyuka akan lokaci kuma bisa ƙa’ida tare da rundunar ganin cewa rundunar ta yi tsayin daka wajen daƙile yunkurin safarar kayayyakin da aka haramta zuwa Najeriya.
“Tun lokacin da na fara aiki a nan, ina ganawa da ƙungiyoyin masu ruwa da tsaki da suka haɗa da masu shigo da kaya, masu fitar da kaya, masu lasisi na aikin fito da masu jigilar kaya, da sauran su, ina mai farin cikin ganin cewa waɗannan tarurrukan suna samun sakamako mai kyau kuma za su ɗore a kwanaki masu zuwa.
“A cikin wannan umarni, muna da al’adar hadin gwiwa tsakanin hukumomi da sauran ƙungiyoyin gwamnati, a cikin wannan watanni uku na farko, na ji daɗin musayar bayanan sirri da tallafi daga sauran hukumomin gwamnati.
“A kan wannan bayanin, ina so in mika godiyata ga shugaban hukumar hana fasakwaɓri ta ƙasa CGC, Kanal Hameed Ibrahim Ali (Murabus) CFR da tawagarsa bisa goyon bayan da suke bayarwa ba tare da gajiyawa ba, tare da godiya ta hukumomin gwamnati a tashar jiragen ruwa ta Apapa don haɗin gwiwa Jami’ai da mutanen Apapa baki ɗaya.” Inji kwanturai AB Mohammed.
Leave a Reply