Take a fresh look at your lifestyle.

WAMAC da MACARTHUR: Taron karfafawa Yan jaridu da bayanai a yaki da cin hanci da rashawa

Nura Muhammed,Minna.

0 211

An bayyana cin hanci da rashawa a matsayin wata ɗabi’a da ke kawo koma baya ga alumma.

 

Shugaban cibiyar wadata and advocacy center WAMAC Alhaji Zubair Abdulrauf shi ne ya bayyana hakan a wani jawabi da ya gabatar a taron da cibiyar tare da hadin gwiwar Gidauniyar Macarthur suka shirya domin karfafa hanyoyin samun bayanai ga Yan jaridu a yaki da cin hanci da rashawa ta yin anfani da harsunan gida a Najeriya.

 

Alhaji Zubair Abdulrauf ya ce cibiyar wadata Media and advocacy center WAMAC da hadin gwiwar Macarthur foundation sun shirya taron ne kan daƙile ɗabi’ar cin hanci da rashawa domin kawo shugabanci na gari a Najeriya ta yin amfani ƙwararrun ‘yan jarida a  harsunan gida domin yaɗa irin illolin ɗabi’ar da cin hanci da rashawa ke yi wa rayuwar alumma.

 

Shugaban cibiyar ta WAMAC ya ce yanzu haka akwai haɗin gwiwa tsakanin wadata Media and advocacy center da Macarthur foundation inda aka ƙulla yarjejeniya da gidajen rediyo goma sha biyu da ke amfani da harsunan gida a shiyoyin kasar shida wajen bayyana irin barnar da cin hanci da rashawa ke yi da kuma  ƙoƙarin ganin an samu shugabanci na gari.

 

Alhaji Zubair Abdulrauf ya ƙara da cewar    “akwai  alaka mai karfe  tsakanin cin hanci da rashawa da  rashin tarbiya wanda hakan ne ke kai ga samar da rashin shugabanci na gari a cikin alumma”.

 

Da take gabatar da ƙasida a taron Hajiya Mairo Mann ta ce dole sai an gyara tarbiya daga gida kafin a kai ga samun shugabanin na gari, saboda a cewarta akwai dangantaka tsakanin rashin tarbiya da cin hanci da rashawa.

 

Hajiya Mairo Mann wadda darakta ce Mai kula ma’amula da zamantakewa a ma’aikatar shari’a a jihar Neja arewa ta tsakiyar Najeriya ta ce “muddin  an son a ga haske a yakin da ake yi da cin hanci da rashawa sai an gyara gida”.

 

Hajiya Mairo Mann ta ce Mafi yawancin matsalolin da ake samu na zamantakewa sune manyan dalilan da ke Sanya a sami rashin tarbiya da zai kaiga haifar da mummunar dabi’a a tsakakkanin alumma.

 

” Da zarar an dai daita sahun gida da yardan Ubangiji komi zai zo da  sauki a rayuwar alumma, amma rashin kula ne ke sanya a Sami alummar da za a rika kuka da ita”.

 

Manyan baƙi da suka  gabatar da jawabi a wajen taron sun harda shugaban kungiyar ‘yan jarida ta ƙasa NUJ  reshen Jihar Neja Abu Nmadu da ma’aikatan gwamnati da sauran shuwagabannin kingiyoyin fararan hula.

 

Take taron na wannan shekarar  shi ne Ƙarfafa bincike bayanan da ke jagorantar aikin jarida a yaƙi da cin hanci da rashawa a cikin harsunan gida a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *