Take a fresh look at your lifestyle.

ABDULSALAM ABUBAKAR YA BUKACI MUSULMAI SU YI AIKI DA DARUSSAN WATAN RAMADAN

Nura Muhammed,Minna.

0 144

Tsohon shugaban mulkin sojan Najeriya Abdulsalam Abubakar ya bukaci alummar musulmai a dukkanin fadin kasar da su yi amfani da darussan da suka koya a lokacin watan azumin Ramadan.

 

 

Abdulsalam Abubakar ya bayyana  hakan ne a lokacin da aka kammala karatun tafsirin Al-ƙur’ani mai girma na watan Ramadan a masallacin da ke gidansa a unguwar Up hill a garin Minna fadar gwamnatin jihar Neja arewa ta tsakiyar Najeriya.

 

 

Tsohon shugaban ya ce akwai bukatar alumma su cigaba da aiwatar da ayyukan ibada da halayya ta gari da suka koya a watan, na yawaita bayar da sadaka da fahimtar juna da girmama abokan zama a ko ina domin ciyar da jihar da ma kasa baki ɗaya.

 

 

Ya ƙara da cewar malamai sun yi iyakar ƙoƙarinsu na ganin sun isar da saƙon da ke  ƙunshe a littattfan addini wanda kuma bin tsarin koyarwar zai taimaka wa alumma samun tsira da Kuma samar da zaman lafiya a garesu.

 

 

Janar Abdulsalam Abubakar ya kuma shawarci  ‘yan Najeriya musamman’ yan siyasa da su hadiye fushinsu kana su haɗa hannu tare don ciyar da kasar gaba.

 

 

Ya ce “An kammala zaɓe,  dole sai an sami damuwa daga bangaran wadanda suka rasa damar, ko Kuma wadanda suka Sami nasara, ni addu’ata nan cewar duk yadda sakamakon ya fito na shari’a sai mu manta da hakan a cigaba da harkoki don ciyar da kasar gaba da nufin farfado da tattalin arzikinmu.

 

 

Tsohon shugaban mulkin sojan ya Kuma shawarci ‘yan takara na jamiyun siyasa daban daban da suka shiga takara da kuma suke ganin ba a yi musu daidai ba, su amince da sakamakon kotu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *