Sojojin Amurka na shirin kwashe ma’aikatan ofishin jakadancin Amurka daga Khartoum babban birnin kasar Sudan.
Kafofin yada labaran Amurka sun ce ana tura sojojin zuwa wani sansanin soji da ke Djibouti.
A halin yanzu, Pentagon ba ta ba da cikakken bayani ba.
Sai dai kuma an yi watsi da yunkurin da wasu kasashe ke yi na kwashe ‘yan kasarsu daga Sudan saboda fargabar tsaro.
Leave a Reply