Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamnatin Najeriya na shirin kwashe ‘yan kasar daga Sudan

0 181

Gwamnatin Najeriya ta ce tana binciko dukkan hanyoyin da za a bi domin ganin an kwashe ‘yan kasarta da suka makale a Sudan tare da dawo da su gida lafiya.

 

Babban Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa, NEMA, Mustapha Ahmed, ya bayyana hakan ne a bisa la’akari da damuwar da ake fama da shi kan lafiyar mazauna Najeriya a Sudan.

 

A cewarsa, hukumar na ci gaba da tattaunawa da dukkan abokan hulda da suka hada da ma’aikatar harkokin wajen kasar, ofishin jakadancin Najeriya da ke Khartoum, Sudan, da hukumar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje da hukumomin tsaro.

 

Ahmed yace; “A halin yanzu halin da ake ciki na gaggawa a Sudan yana da sarkakiya tare da fada tsakanin bangarorin da ke rikici da juna kuma an rufe dukkan filayen tashi da saukar jiragen sama da kan iyakokin kasa.”

 

Yace; “Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa, NEMA tana aiki tukuru tare da dukkan abokan huldarta kuma tana tattara sabbin bayanai kan lamarin.”

 

Ahmed ya kara da cewa, “An kafa wani kwamiti wanda ya kunshi kwararrun masu ba da agajin gaggawa, kwararrun bincike da ceto don tantance halin da ake ciki akai-akai tare da lalubo hanyar da ta fi dacewa ta kwashe ‘yan Najeriya ko da ta wata kasa makwabciyarta Sudan.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *