Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rantsar da sabbin sakatarorin dindindin guda shida da aka nada.
An gudanar da bikin rantsarwar ne a safiyar ranar Laraba a zauren majalisar da ke fadar shugaban kasa ta Villa, Abuja.
Wadanda aka rantsar sune; Adam Kambari daga jihar Borno, Esuabana Asanye, jihar Kuros Riba; Lamuwa Adamu Ibrahim, Jihar Gwambe; Yakubu Adamu, Jihar Kano; Oloruntola Micheal, Jihar Ogun; da Richard Pheelangwah, Jihar Taraba.
Bikin ya gudana ne gabanin taron mako-mako na Majalisar Zartaswa da ke gudana yanzu haka a zauren majalisar da ke fadar shugaban kasa ta Villa Abuja.
Wadanda suka halarci taron sun hada da sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha; Shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Dr Folasade Yemi-Esan; da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya.
Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da ministar kudi, kasafin kudi, da tsare-tsare ta kasa, Zainab Ahmed; Babban Lauya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami; da na Babban Birnin Tarayya (FCT), Mohammed Musa Bello, da sauransu.
A zantawar ta da manema labarai na fadar gwamnatin jihar, shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Dakta Folashade Yemi-Esan ta bukaci sabbin sakatarorin dindindin da su bayar da dukkan gudunmawar su wajen gudanar da ayyukansu.
Leave a Reply