Majalisar dokokin Jamus ta ba da haske kan batun tura sojoji Nijar.
Sojojin Jamus 60 ne za su shiga tawagar Tarayyar Turai da aka kafa a watan Disambar da ya gabata da nufin taimakawa kasar wajen inganta kayan aiki da kayayyakin more rayuwa.
Matakin da majalisar dokokin kasar ta dauka a birnin Berlin na kara tabbatar da ci gaba da zaman Jamus a yankin Sahel duk da janyewar kasar daga Mali.
Nijar dai na fuskantar barazanar tashe-tashen hankula da ke kunno kai daga makwabciyarta Mali inda mayakan ke ci gaba da samun galaba bayan janyewar sojojin Faransa da na wasu kasashen Turai.
Leave a Reply