Take a fresh look at your lifestyle.

Hasashen Tattalin Arziƙin Duniya Na Iya Raguwa Da Kashi 7% – IMF.

Aisha Yahaya, Lagos

1 432

Asusun Ba da Lamuni na Duniya IMF,ya ce, hasashen tattalin arzikin duniya zai iya raguwa da kashi 7%, idan tattalin arzikin duniya ya yay i sanadiyar rarrabuwar kawuna ,bayan shekaru da dama .

 

 

 

A wani sabon rahoton ma’aikata IMF tace asarar na iya kaiwa kashi 8-12% a wasu kasashe, idan har aka lalata fasaha.

 

 

 

Asusun na IMF ya ce ko da takaitaccen rarrabuwar kawuna na iya aske kashi 0.2% na GDP na duniya, amma ta ce ana bukatar karin aiki don tantance kudaden da ake kashewa ga tsarin hada-hadar kudi na kasa da kasa da kuma cibiyar kare kudi ta duniya (GFSN).

 

 

 

Sanarwar da aka fitar a yammacin Lahadin da ta gabata, ta yi nuni da cewa, hauhawar kayayyaki da jari a duniya ya yi kamari bayan rikicin kudi na duniya na 2008-2009, da karuwar takunkumin cinikayya da aka samu a shekarun baya.

 

 

 

Rahoton ma’aikatan ya ce “Cutar COVID-19 da kuma mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine sun kara gwada dangantakar kasa da kasa da kuma kara nuna shakku game da fa’idar dunkulewar duniya.”

One response to “Hasashen Tattalin Arziƙin Duniya Na Iya Raguwa Da Kashi 7% – IMF.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *