Rundunar Tsaron Hadin Gwiwa ta Jihar Anambra ta tarwatsa wata masana’antar bamabamai ta boye tare da dakile wasu bama-bamai da dama a wani samame da suka kai a wata maboyar ‘yan aware a garin Isseke da ke karamar hukumar Ihiala ta jihar.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Anambra, DSP Tochukwu Ikenga ya fitar ranar Lahadi, ya bayyana wurin a matsayin daya daga cikin wuraren da suka rage a hannun ‘yan awaren a jihar.
A cewar sanarwar, wurin ya kasance wani katafaren sansani sama da shekaru biyu kuma ana zargin an yi amfani da shi wajen shiryawa da aiwatar da munanan hare-hare a fadin yankin.
Ikenga ya ce, an aiwatar da aikin ne a ranar Asabar, 24 ga watan Mayu, ta hanyar hadin gwiwar jami’an tsaro da suka hada da rundunar ‘yan sandan Najeriya, da sojoji, da kuma jami’an hukumar ‘yan banga na jihar Anambra.
“Tawagar jami’an tsaro ta hadin guiwa ta kai farmakin na ta zuwa wani maboyar ‘yan ta’adda da ke Isseke, a karamar hukumar Ihiala. A yayin farmakin, an lalata wata masana’antar bama-bamai a cikin gida, an kuma gano wasu bama-bamai da aka kera a cikin gida, kuma an lalata su cikin koshin lafiya,” in ji Ikenga.
Ya kara da cewa, daya daga cikin bama-baman da aka binne ta tarwatse a yayin farmakin, inda ta yi barna sosai ga wata titin da ke kusa da wurin, tare da zama tarkon baragurbi domin dakile ci gaban jami’an tsaro.
Duk da tsananin aikin da bama-baman ke yi, Ikenga ya tabbatar da cewa ba a samu asarar rai ba.
Ya kara da cewa jami’an tsaro na ci gaba da gudanar da ayyukansu a yankin a ci gaba da kokarin kwato yankin gaba daya daga hannun ‘yan Ta’adda.