Take a fresh look at your lifestyle.

Kungiyar RedCross za ta kai wa Kano tallafi kan cutar Mashako

Yusuf Bala Nayaya,Kano.

0 224

Kungiyar agaji ta kasa da kasa RedCross za ta tallafa wa al’ummar jihar Kano Arewa maso Yammacin Najeriya  don yakar cutar mashako da ke haifar da sarkewar numfashi da makogwaro ta Diphtheria.

 

 

Jihar dai ta kasance cikin na gaba-gaba inda wannan cuta ta yi kamari a Najeriya don haka Kungiyar ta Redcross ta bayyana cewa ta shirya tsaf don ilimantar da jama’a kan yadda za su kare kansu daga wannan cuta ta mashako da ake kira da Diphtheria a Turancin Ingilishi.

 

 

Musa D. Abdullahi shine babban sakataren kungiyar ta RedCross reshen jihar ta Kano yace kungiyarsu da hadin gwiwa da maaikatar lafiya ta jihar Kano sun shirya gabatar da bita tsawon watanni uku ga al’ummar jihar ta Kano duba da yadda wannan cuta ke kara kamari a jihar.

 

“Mune muke da mafi yawan alkaluma na mutane da aka tabbatar sun kamu da wannan cuta ta Dephtheria . Don haka a kananan hukumomi 11 da za mu gabatar da wannan aiki na fadakar da jama’a. A kowace karamar hukuma mun samu mutane 20 mata 15 maza 5 amma a karamar hukumar Ungoggo da ke kan gaba da yawan masu fama da wannan cuta mun ware mutane 50, mata 45 maza 5.”

 

 

A cewar Musa D. Abdullahi  babban sakataren kungiyar ta Redcross reshen jihar ta Kano sun zabi mata da yawa sama da maza don gudanar da wannan aiki kasancewar mata su za su iya shiga gida-gida don fadakar da al’umma musamman iyaye mata kan yadda za su kula da tsafta dama kulawa da kayan abinci. Su kuwa maza su za su je kasuwanni ko makarantu ko wajen wani gangami don fadakar da al’umma.

 

 

Har ila yau Musa D. Abdullahi ya kara da cewa:

“Akwai ma’aikata a kowace karamar hukuma, ba za a dauki wasu daga wata karamar hukuma a kaisu wata ba, kuma za a yi allurai na rigakafi  baya ga fadakarwar.”

 

 

Sakataren na RedCross a Kano ya ce a mako mai zuwa ne jami’an hukumar ta RedCross a matakin kasa tare da na Hukumar Lafita ta Duniya WHO daga Abuja da jami’an ma’aikatar lafiya ta jihar Kano za su zauna a Kano don tattaunawa kan yadda za su gudanar da aikin nasu.

 

Abdullahi y ace kungiyarsu ita ke da kwarewa wajen bada horo na agajin gaggawa kamar yadda yake tsakanin kasa da kasa don haka ne ma ita ke ba da horo ga ‘yansanda da sojoji da jami’an kashe gobara da dai sauransu inda suke basu takardar shedar sun kware a aikin ko akasin haka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *