Take a fresh look at your lifestyle.

Kifewar Kwale-kwale Ya Hallaka Mutum 15 A Sokoko

Shehu Salman, Sokoto

0 239

Mutane goma shabiyar ne suka rasa rayukansu Sakamakon kifewar wani Kwalekwale a jihar Sokoto.

A cikin waɗanda suka rasa rayukan nasu sun haɗa da mata 2 da su ke ƙoƙarin tsallaka wani katafaren Dam daga ƙauyen Lambara zuwa ƙauyen mashayar Dundeji a cikin ƙaramar hukumar mulki ta Shagari da ke jihar Sokoto arewa maso yammacin Najeriya.

Wasu shedun gani da ido sun shaidawa muryar Najeriya cewa Dam ɗin ya jima ya na laƙume rayuwar al’ummar yankin kusan ko wace shekara.

Gwamnatin jihar ta Sokoto ta sha ɗaukar alƙawuran shawo kan wannan balahira amma shiru kake ji a cewar mutanen yankin.

Kimanin mutane goma sha biyar ne suka rasa rayukansu inda wasu Shirin da biyar su ka yi batan dabo yayin hatsarin kwale-kwalen.

Abdulkarim Rabiu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *