Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Najeriya, NEMA, ta aike da kayan abinci iri-iri da aka amince da su ga ofishin jakadancin Najeriya a Sudan don daukar nauyin ‘yan Najeriya da ke jiran jigilar jiragen sama a Port Sudan da ke dawowa gida daga Sudan da yaki ya daidaita.
Kayayyakin abincin, a cewar Darakta Janar NEMA Mustapha Ahmed, ya ce an dauki wannan matakin ne domin ciyar da ‘yan Najeriya abinci yayin da ake ci gaba da aikin kwashe mutanen.
” Kayayyakin sun kunshi buhu 100 na shinkafa kilogiram 10, buhun wake 10kg 50, katon kayan yaji guda 10, katon spaghetti 50 da kuma buhunan gishirin iodized buhu 5.
“Tarco Aviation ne ya kwashe kayayyakin a ranar Alhamis zuwa Port Sudan wanda a baya ya kawo ‘yan Najeriya 123 da suka makale zuwa Abuja.
Ahmed ya kara da cewa: “Sabo da zuwan na baya-bayan nan ya kawo adadin ‘yan Najeriya da suka makale zuwa 2,246 a cikin jirage 12 daban-daban.
Dole ne a nanata cewa ana ci gaba da aikin kwashe mutanen tare da kokarin hada wasu kamfanonin jiragen sama na Najeriya don karfafa jigilar jiragen Najeriya da ke son dawowa gida daga Sudan.
Leave a Reply