Gwamnan jahar Neja dake arewa ta tsakiyar Najeriya Abubakar Sani Bello ya nada mai martaba sarkin Borgu Alhaji Mohammed Sani na VI a matsayin Amirul Hajj na jahar na shekara ta 2023.
Sakon hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataran gwamnatin jahar Alhaji Ibrahim Matane ya fitar aka rabawa manema labarai a garin Minna fadar gwamnati jahar Neja.
Sauran mambobin tawagar Amirul Hajj da gwamnatin ta nada sun hada da Injiniya Mohammed Sulaiman da Alhaji Shehu Yahaya da yarima Musah Madaki da ke kasancewa sakataran tawagar.
Ana shi bangaran shugaban hukumar jin dadi alhazan jahar Alhaji Muhammad Awwal ya taya sabon Amirul Hajjin murnar samun matsayin, inda ya kuma baiwa jagoran da sauran yan tawagarsa tabbacin hukumar na hadin kai don ganin komi ya tafi kamar yadda aka tsara.
Alhaji Muhammad Awwal ya kuma kara da cewar tuni hukumar ta kammala dukkanin shirye shiryenta na fara aikin da ya rataya a wuyanta domin kaucewa shiga rudani a yayin aikin hajjin.
Leave a Reply