Take a fresh look at your lifestyle.

An Yaba Wa Shugaba Buhari Kan Nadin Daraktocin Hukumar Bunkasa Arewa Maso Gabas

Musa Aminu, Abuja

0 231

Kungiyar Manoman kaji na kasa reshen Abuja babban birnin Najeriya ta yabawa shugaban kasar Muhammadu Buhari bisa nadin daraktocin hukumar bunkasa yankin Arewa maso gabashin Najeriya, wato North East Development Commission a turance, shugaban kungiyar Mista Pius Aminu ya bayyana nadin Barasta Bashir Bukar Ba’ale a matsayin daya daga cikin daraktocin da shugaba Buhari yayi abun a yaba kwarai maruka.
A cewar Mista Pius, Barasta Bashir Mutum ne dake da kwarewa tare da kwazo a farnoni daba-daban na rayuwa kuma yana da yakinin cewa zai yi amfani da kwarewarsa wajen ciyar da yankin dama kasa baki daya zuwa mataki na gaba.

Buga kari, kungiyar ta Manoman kaji ta bukaci daukacin al’umomin da suka fito daga yankin Arewa maso gabashin Najeriya da cigaba da baiwa hukumar ta bunkasa yankin goyon baya domin samun cigaban yankin dama na kasa baki daya.

Idan dai za iya tunawa a farkon watan mayun da muke ciki ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada daraktocin gudanarwar kuhumar bunkasa yankin Arewa maso gabashin Najeriya biyo bayan kammala tantace su da Majalisar dattawan kasar ta yi kamar yadda doka ta tanadar.

Abdulkarim Rabiu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *