Take a fresh look at your lifestyle.

Majalisar Dattawa Ta Jaddada Kudirinta Na Habbaka Hanyoyin Samun Kudaden Shiga A Najeriya

Abdulkarim Rabiu, Abuja

0 195

Majalisar Dattawan Najeriya ta jaddada kudirinta na karfafa hanyoyin samar da kudaden shiga a kasar ta hanyar inganta kwazon kwararru a fannin ilimin haraji.

Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawn shi ne ya tabbatar da hakan a lokacin da yake bude taron jin ra’ayin jama’a na yini daya kan kudirin kafa kwalejin nazari Ilimin haraji da harkokin kudi a Najeriya.

Shugaban majalisar dattijai wanda Sanata Aliyu Sabi Abdullahi ya wakilta ya bukaci masu ruwa da tsaki da su saki jikinsu, su bada da gudunmawa a abubuwan da kudirin ya kunsa domin majalisar ta samu damar Samar da dokokin da suka dace wadanda za su inganta fasahar samar da kudaden shiga na kasar.

Ya ce bunkasa ilimi da kwarewar dan Adam mabudi ne wajen samun ci gaba mai dorewa da karfin tattalin arzikin kowace al’umma.

A jawabinsa na bude taron shugaban kwamitin majalisar dattawa Mai kula da ayyukan gwamnati, Sanata Ibrahim Shekarau ya shawarci masu ruwa da tsaki da su yi bayanin abin da suke ganin ya dace kwamitin ya yi aiki da shi wajen tattara rahotannin sa domin nazarin majalisar dattawa baki daya.

Ya ce sauraron ra’ayin jama’a wani muhimmin tsari ne na samar da dokoki masu ma’ana wadanda suka shafi rayuwar kowa a kowane tafarkin dimokuradiyya, don haka akwai bukatar bayar da kwakkwarar gudunmawa daga masu ruwa da tsaki.

Da yawa daga cikin masu ruwa da tsaki kamar cibiyar nazarin tattara haraji wato Charted Institute of Taxation da Hukumar Jami’o’i ta Kasa sun goyi bayan kudurin amma sun yi kyakkyawan nazari da ya kamata a yi aiki da su kafin sanya kudirin dokar ya zama doka mai inganci.

Da yake mayar da martani kan hakan, dan majalisar dattijai Sanata Aliyu Sabi Abdullahi ya bukace su da su bayar da gudunmawar da suka dace domin kudurin ya zama doka mai ma’ana.

Sanata Sabi ya jaddada cewa ya yi tunanin samar da dokar kafa kwalejin ne a lokacin da ya lura da bukatar karfafa abubuwan da ake bukata na ilimi don bunkasa kwarewar aiki tare da manufar inganta bangaren haraji da kuma samar da kudaden shiga na kasar, ra’ayin da hukumar tattara haraji ta kasa ta goyi bayan.

Abdulkarim Rabiu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *