Hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya, NDLEA, ta kama wasu masu safarar miyagun kwayoyi 185 a gidajen sayar da muggan kwayoyi daban-daban a Abuja, babban birnin Najeriya da kuma Kano, cibiyar kasuwancin Arewa.
Jami’an Hukumar sun kwace magunguna kala-kala daga hannun masu safarar miyagun kwayoyi a cikin ayyukan da suka yi a makon jiya.
Wata sanarwa da kakakin hukumar Mr. Femi BabaFemi a Abuja ya ce, jami’an NDLEA ma sun kama wasu ‘yan kasuwa guda biyu a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe International Airport Abuja bisa laifin shan hodar iblis.
Baba Femi ya ce, dukkansu sun fitar da kwalayen haramun guda 193 bayan kwana uku a tsare.
“Masu fataucin: Onoh Ebere, mai shekaru 49, da Christian Ifeanyi Ogbuji, mai shekaru 47, an kama su a filin jirgin saman Abuja a ranar Laraba, 10 ga watan Mayu bayan da suka taso daga Uganda ta hanyar Addis Ababa, cikin jirgin Ethiopian Airlines ET 951.”
Jami’an yaki da safarar miyagun kwayoyi sun damke masu safarar miyagun kwayoyi tare da kama wasu haramtattun kwayoyi a jihohin Legas, Ogun, Taraba, Borno, Filato da Anambra.
Yayin da yake yaba wa jami’an hukumar da abin ya shafa bisa jajircewarsu, babban jami’in hukumar ta NDLEA, Brig. Gen. Mohamed Buba Marwa ya bukaci su da takwarorinsu a fadin kasar nan da su kara kaimi wajen samar da magunguna da ayyukan rage bukatun muggan kwayoyi.
Leave a Reply