Take a fresh look at your lifestyle.

Hajji: Hukumar Jin dadin alhazan Jihar Neja ta bada tabbacin jigilan alhazan jahar

Nura Muhammed,Minna.

0 199

Alhaji Muhammad Awwal Aliyu  ya baiwa alummar jahar tabbacin fara jigilar alhazan zuwa kasa Mai tsarki bisa jaddawalin  hukumar hajji ta kasa NAHCON ta tsara.

 

Alhaji Muhammad Awwal Aliyu ya ce hukumar ta kammala dukkanin shirye shiryen na ganin an fara dibar maniyatan zuwa kasa Mai tsarki, inda ya bukace su da su halarci Taron horaswa  da ake yiwa maniyata a dukkanin fadin kasar don ya taimaka masu sanin dokoki da Kuma ka’idojin aikin hajji.

 

Shugaban hukumar ya Kuma bukaci maniyata aikin hajjin bana daga jahar da su kasance masu bin ka’idojin da dokokin na  kasar Saudiya, inda ya ce hukumar Hajji ta kasa ta tsara yadda za’a Kwashe  alhazan jahar da ma kasa Baki Daya.

 

Hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta zabi jiragen Saman Saudiya a matsayin jiragen da zai Kwashe alhazan jahar Neja a aikin hajjin bana na shekara ta 2023 a cikin wannan watan da muke ciki.

 

 

Nura Muhammed,Minna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *