Majalisar wakilan Najeriya ta dage zamanta zuwa ranar Alhamis, bayan rasuwar wani mamba mai ci daga jihar Edo, Jude Ise-Idehen.
Shugaban majalisar, Femi Gbajabiamila, ya yi addu’ar Allah ya jikan dan majalisar.
A wata wasika da ya aike wa majalisar rasuwar Jude Ise-Idehen, daya daga cikin ‘yan majalisar, Omoregie Ogbeide-Ihama, ya ce za a yi kewar gudunmawar da ya bayar.
Leave a Reply