Take a fresh look at your lifestyle.

SHUGABAN NAJERIYA YA JINJINA WA KUNGIYAR KWALLON KAFA TA MATAN NAJERIYA

0 212

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jinjina wa kungiyar kwallon kafa ta mata Super Falcons a karawar su da takwarar su ta Maroko a was an zagayen karshe na gasar cin kofin kwallon kafa na matan Afirka.

‘‘Koda yake alumma da dama basuji dadin nasarar da kungiyar matan Maroko sukayi ba a bugun daga kai sai mai tsaron gida,wannan zai baiwa kungiyar Najeriya shirya tunkarar wasanin da zaa buga nan gaba,’’ inji Shugaban kasa.

A sakon da ya aika wa kungiyar Falcons, Shugaba Buhari yace yana mai jinjina wa irin kwazo,juriya da kwarewar wasa da ‘yan Matan suka nuna,duk kuwa da cewa an cire ‘yan wasa biyu.

Yayi ammana cewa nan gaba kungiyar kwallon kafa ta matan Najeriya zasu taka rawar gani a wasannin da zasu buga nan gaba.

LADAN NASIDI

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *