Take a fresh look at your lifestyle.

SHUGABA BUHARI YA SANYA BAKI A YAJIN AIKIN KUNGIYAR ASUU

0 156

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya baki a yajin aikin da kungiyar Malaman Jamio’I ta Najeriya take ciki da yaki ci yaki cinyewa.

Ya gana da wasu Ministoci da hukumomin da abun ya shafa a ofishin shi ranar Talata domin shawo kan yajin aikin day a dauki tsawon lokaci.

Jamian Gwamnati dake kokarin ganin an kawo karshen yajin aikin,sun yi wa Shugaba Buhari bayanai.

Daha cikin wadanda suka halarci taron hard a Sakataren Gwamnatin Najeriya, Boss Mustapha, Ministan Ilimi, Adamu Adamu, Ministan Kudi,Kasafin kudi da Tsare Tasare, Zainab Ahmed, Ministan Kwadago da samar da aikin yi, Dr Chris Ngige, Ministan Sadarwa da harkar Naura r zamani Mai Yatsu, Isa Pantami, Shugabar Maaikatan Gwamnatin Tarayya, Dr. Folashade Yemi-Esan, Ben Akabueze.

Tun ranar 14 ga watan Feburairu kungiyar malaman Jamio’I ta Najeriya ASUU ta tsunduma yajin aiki na jan kunne,sauran kungiyoyi suka bi sahun ta inda suke bukatar Gwamnatin tarayya ta biya musu bukatun sun a hakkokin day a akayi yerjejeniyar zata biya su.

Sauran kungiyoyin da suka bi sahun ASUU, hard a kungiyar maaikatan Jamio’I,SSANU,manyan maaikata da ba malamai baa Jamio’i, NASU da Kungiyar malaman kimiya da fasaha, NAAT.

LADAN NASIDI

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *