Kungiyar direbobin mota masu dakon kaya a jihar Kano Arewa maso Yammacin Najeriya ta yi gargadi ga mambobinta su guji daukar baki ‘yan kasashen waje da ke shigawa Kano ba bisa ka’ida ba.
Gargadin kungiyar na zuwa ne bayan da aka gano cewa bakin na sauya hanyoyi da suke shiga Najeriya ko ma jihar ta Kano ta barauniyar hanya.
Sakataren kungiyar motocin dakon kayan Malam Abubakar Suleiman da yake zantawa da manema labarai a jihar ta Kano ya bayyana cewa hukumar da ke kula da shige da fice a jihar ta Kano ita ta ankarar da su cewa kawo yanzu suna samun baki da ke shiga jihar ta Kano ta hanyar hawa motocin dakon kaya sabanin yadda a baya aka saba zakulo su a motocin bas-bas ko manyan motocin sufurin al’umma da ke kira Luxurious bus a Turance.
A cewar Malam Suleiman aikin fadakarwar tasu bai tsaya ga dakile fasakaurin mutanen ba har ma da tallafawa hukumar da ke hana fasakaurin kayayyaki da aka haramta wato Kwastam ta yadda suke fadakar da mambobinsu su guji daukar kaya da aka haramta a dokokin kasa, don kada su sa kansu a cikin matsala.
Sakataren kungiyar masu motocin dakon kayan Abubakar Suleiman ya kuma kara da cewa kungiyar su ta kan kuma fadakar da mambobinsu su zama masu bin doka da oda kan duk wasu dokoki da suka shafi tuki dama daukar kayan ta yadda za su ba da tasu gudunmawa wajen tsaftace harkokin dakon kaya da ma ba da tasu gudunmawa don ciyar da jihar ta Kano gaba.
Leave a Reply