Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a jihar Kano ta soke takarar zababben gwamnan jihar Abia, Dr Alex Otti.
Kotun da ke karkashin Mai shari’a M N Yunusa ta kuma soke takarar duk wasu masu rike da tutar jam’iyyar Labour a jihohin Abia da Kano.
KU KARANTA KUMA: Alex Otti ya lashe zaben gwamnan jihar Abia
Yunusa ya yanke hukuncin cewa fitowar su bai dace da tanadin dokar zabe ta 2022 ba.
Alkalin ya yanke hukuncin ne a kan karar mai lamba FHC/KN/CS/107/2023 da wani Mista Ibrahim Haruna Ibrahim ya shigar a kan jam’iyyar Labour da kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa.
KU KARANTA: An yi murna a jihar Abia yayin da Alex Otti ya zama zababben gwamnan jihar
“Jam’iyyar da ba ta bi tanade-tanaden dokar zabe ba, ba za a ce tana da dan takara a zabe kuma ba za a iya bayyana ta a matsayin wadda ta lashe zabe ba; saboda haka, kuri’un da aka baiwa wanda ake kara na 1, kuri’a ce ta bata,” inji alkalin.
L.N
Leave a Reply