Take a fresh look at your lifestyle.

Dan Majalisa Yayi Kiran Samar Da Doka ta Musamman Don Haɓaka Masana’antar Kula Da Baƙi

0 183

Sanata Orji Uzor Kalu ya yi kira da a samar da doka ta musamman da za ta taimakawa kananan ‘yan kasuwa musamman masu karbar baki wajen samun lamuni a Najeriya.

 

 

Kalu ya yi wannan kiran ne a Abuja a lokacin kaddamar da gidan cin abinci na Tastia da kuma gidan burodi a Wuse 2, cibiyar kasuwanci ta babban birnin kasar.

 

 

Ya ce “akwai bukatar a kara karfafa gwiwar matasa ‘yan kasuwa masu samar da rance a kokarinsu na rage rashin aikin yi a kasar.”

 

 

Ya yi kira ga gwamnati da ta samar da yanayi mai kyau da kuma samar da wani banki na musamman ga masu kananan sana’o’i don samun lamuni mai sauki.

 

 

A cewarsa, mutanen da ke fitar da matasa marasa aikin yi daga tituna, da inganta harkokin kasuwanci a kasar na bukatar karfafawa da tallafa musu.

 

 

“Muna bukatar mu fito da sabbin dokoki don karfafa gwiwar ‘yan kasuwa da kuma kare harkokin kasuwancinsu. Ya kamata gwamnati ta kuma yi la’akari da kafa bankin karbar baki domin samar da damammaki ga wadanda ke sana’ar karbar baki domin samun lamuni,” inji Sanata Kalu.

 

Ya yi kira da a samar da karin dokoki don inganta yanayin kasuwanci, don bunkasa zuba jari mai zurfi a ciki da wajen kasar nan.

 

 

A nasa bangaren, mamallakin gidan cin abinci na Tastia Restaurant and Bakery, Mista Kester Agwu ya ce akwai bukatar gwamnati mai zuwa ta bullo da tsare-tsare don bunkasa harkokin kasuwanci.

 

 

Agwu ya bayyana cewa ya dauki ‘yan Najeriya 1000 aikin karbar baki kuma zai ci gaba da bude wasu rassa a fadin kasar da nufin samar da ayyukan yi ga jama’a.

 

 

Ya kara da cewa ya fadada harkokin kasuwanci domin tallafawa kokarin gwamnati na rage rashin aikin yi a kasar.

 

 

L.N

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *