Take a fresh look at your lifestyle.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi nadamar korar kakakinta a Mali

0 246

Tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Mali, MINUSMA ta ce ta yi nadamar korar kakakinta. Gwamnatin Mali ta umurci Mataimakin Babban Jami’in Sadarwa da Kakakin Majalisar Dinkin Duniya, Olivier Salgado da ya fice daga yankin nan da kwanaki uku saboda kalaman ‘marasa karbuwa’ game da kame wasu sojojin Ivory Coast da dama a Bamako. Kokarin wanzar da zaman lafiya Mista Salgado ya ce an sanar da kasar Mali zuwan sojojin Ivory Coast, wadanda gwamnatin mulkin sojan kasar ke zarginsu da kasancewa ‘yan amshin shatan haya’ da ke shirin kawo rashin zaman lafiya a kasar. Kasar Mali ta dakatar da aikin dakarun na MINUSMA jim kadan bayan haka kuma ta hana sojoji takwas daga cikin dakarun Jamus barin Bamako. Dangantaka mai cike da rudani tsakanin sojojin Mali da tawagar Majalisar Dinkin Duniya na barazanar kawo cikas ga ayyukan wanzar da zaman lafiya da kuma kara tabarbarewar zaman lafiyar kasar. A ranar 29 ga watan Yuli ne ake sa ran wata fitacciyar kungiyar fafutuka mai rajin ra’ayin Rasha, Yerewolo sur les Remparts, za ta gudanar da zanga-zangar kin jinin Minusma, a daidai lokacin da kasar Mali ke bikin ranar samun ‘yancin kai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *