Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS, ta ce tana bibiyar al’amuran da ke faruwa a jamhuriyar Bolivaria ta Venezuela da matukar damuwa.
Sanarwar da hukumar ECOWAS ta fitar ta ce, yayin da ta amince da ‘yancin da kasashe ke da shi na yaki da laifukan kasa da kasa da suka hada da ta’addanci da safarar miyagun kwayoyi, hukumar na fatan tunatar da al’ummar duniya “wajibinsu na mutunta ‘yancin kai da yankin juna”, kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tanada.
Karanta kuma: Trump ya kawo karshen mulkin Maduro a Venezuela
Paparoma Leo yayi kira ga Ci gaba da ‘Yancin Venezuela
Sanarwar ta kara da cewa: “ECOWAS ta yi daidai da furucin kungiyar Tarayyar Afirka da ke kira da a kame tare da yin tattaunawa a tsakanin al’ummar Venezuela.”
Hukumar ta ECOWAS ta sake nanata “hadin kai tare da al’ummar Venezuela tare da yin kira ga dukkan Jihohin da su mutunta ‘yancin kai da kuma yankunan Venezuela” tare da bayyana goyon bayanta ga al’ummar kasar yayin da suke tsara makomar kasarsu ta hanyar da ta dace.
Aisha Yahaya Lagos