Babban sakataren majalisar ministocin kasar Japan Hirokazu Matsuno ya ce kasar za ta kakabawa Rasha karin takunkumi bayan taron kungiyar G7 da kasar ta karbi bakunci a makon da ya gabata ya amince da daukar matakan hukunta mamayar da Moscow ta yi wa Ukraine.
A cewar sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen kasar Japan ta fitar a jiya Juma’a, Japan a wani mataki na hadin gwiwa tare da G7, za ta dakatar da kadarorin kungiyoyi 78 da wasu mutane 17 ciki har da jami’an soji a Rasha tare da hana fitar da kayayyaki zuwa wasu sassan Rasha 80 kamar dakunan binciken da ke da alaka da soja.
Sanarwar da ma’aikatar cinikayya ta fitar ta ce, kasar Japan za ta kuma haramta ba wa Rasha ayyukan gine-gine da injiniyoyi, ko da yake za a sanar da cikakken bayanin matakin nan gaba.
Matsuno, babban mai magana da yawun gwamnatin Tokyo, ya kuma yi Allah wadai da matakin da Rasha ta dauka a ranar Alhamis na tura makaman kare dangi a Belarus, yana mai cewa hakan zai kara tsananta halin da ake ciki game da mamayewar Ukraine.
Hakanan Karanta: Japan ba za ta shiga NATO ba – PM Kishida
Matsuno ya shaida wa taron manema labarai na yau da kullun cewa, “A matsayin kasa daya tilo da ta fuskanci hare-haren nukiliya a lokacin yaki, Japan ba ta taba amincewa da barazanar nukiliyar Rasha ba, balle a yi amfani da ita.”
Shugabannin kasashen G7 da suka hada da Amurka da Birtaniya da Jamus da kuma Faransa a makon da ya gabata sun nuna aniyarsu ta tallafa wa Ukraine da karin taimakon soji da kuma takunkumi kan kasar Rasha, a taron shekara-shekara da ake gudanarwa a birnin Hiroshima na farko a duniya da aka kai harin bam.
Leave a Reply