Gwamnan jihar Neja dake arewa ta tsakiyar Najeriya Umar Mohammed Bago ya bukaci hadin kai daga al’ummar jihar domin ya sami damar aiwatar da ayyukan raya kasa.
Gwamnan ya bayana hakan ne a jawabin sa na farko bayan Shan rantsuwa kama aiki a matsayin sabon Gwamnan jihar a filin dandalin kasuwar duniya dake garin Minna.
Gwamna Umar Mohammed Bago ya ce jihar nada kalubale da dama da yakamata a maida hankali a kan su domin ciyar da jihar gaba ta yakar talauci.
Sabon Gwamnan ya ce zai maida hankali sosai kan matsalar tsaro ganin yadda ake fama da rashin tsaro a dukkanin fadin jahar, inda ya ce dole sai ya sami hadin Kai daga alummar jihar wanda hakan ne zai bashi damar samun nasara kawo karshen matsalar.
Gwamna Umar Mohammed Bago ya Kara da cewar zai Kuma “inganta bangaran shakatawa a jahar duba ga irin yadda ake da mahimman kayayyakin tarihin a jahar ta hanyar gayyato masu zuba jari da sauran hanyoyin cigaba ga jihar da alummar ta.”
Hakazalika, ganin irin mahimmanci dake tattare da sashen kiwon lafiya, sabon gwamnan ya ce zai “inganta bangaran, inda zai daga martabar manyan asibitocin da ake da su a jihar da sauran kananan cibiyoyin kiwon lafiya.”
Gwamnan ya Kuma ce zai “himmatu wajan ganin jihar ta wadatu da wutan lantarki domin anfanin yan jahar da ma makwabta.”
Ya kara da cewa “gwamnatin sa zata farfado da cibiyoyin koyar da sana’oi ga matasa da Kuma farfado da masana’antu da suka durkushe a jahar domin samarwa da matasa ayyukan Yi.”
A karshe gwamna Umar Mohammed Bago ya godewa tsoffin Shuwagabanin kasa Ibrahim Badamasi Babangida da Abdulsalam Abubakar bisa shawarwari da Kuma goyan baya da suka bashi da kuma alummar jihar bisa ammar da suka bashi na zama shugaban su, ya Kuma sha alwashin gudanar da ayyukan raya kasa domin inganta rayuwar alummar jihar Neja.
Gwamnan ya Kuma yabawa sarakunar jahar karkashin shugaban sarakunan Alhaji Dr Yahaya Abubakar bisa goyan bayan su na ganin jihar ta cigaba.
Babban alkalin alkalan jahar ya Sha rantsuwa ne Babban alkalin alkalan jihar Neja Mai shari’a Halima Ibrahim Abdulmalik ta rantsar da Umar Mohammed Bago bayan nasarar da ya samu a babban zaben jihar a watan maris na wannan shekarar da muke ciki.
Leave a Reply