Take a fresh look at your lifestyle.

Hukumar Talabijin ta Najeriya Ta Samu Sabbin Daraktoci

0 394

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin da aka mika masa domin amincewa da shi a matsayin manyan daraktocin gidan talabijin na Najeriya, NTA bayan tafiyar masu rike da mukaman, wadanda wa’adinsu ya kare a ranar 31 ga watan Maris.

Wadanda aka nada a sabbin mukaman sune:

1. Ije Osagie (Jihar Edo) Babban Daraktan Injiniya

2. Betsy Iheabunike (Jahar Anambra) Babban Daraktar Talla

3. Lawal Umar Lalu (Katsina) Babban Daraktan Shirye-shirye

4. Ayo Adewuyi (Jihar Osun) Babban Daraktan Labarai

5. Adamu Sambo (Jihar Adamawa) Babban Daraktan Ayyuka na Musamman

6. Nansel Nimyel (Jihar Plateau) Babban Daraktan Gudanarwa da Horarwa

7. Abdullahi Ismail Ahmed (Kaduna) Babban Daraktan Kudi.

Wadanda aka nada za su yi aiki na shekaru uku na farko, za a sabunta su na wasu shekaru uku kuma nadin ya fara aiki daga Mayu 26, 2023.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *