Take a fresh look at your lifestyle.

Gaggauta Zuwa Asibiti Yayin Nakuda Zai Magance Yoyon Fitsari

Shehu Salmanu

125

Zuwa asibiti da zarar an fara nakuda ne kawai zata kawar da matsalar yoyon fitsari.

Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar 23 ga watan Mayu ta kowace shekara domin fadakarwa da wayar da kan mutane game da matsalar yoyon fitsari, al’ummar jihar Sokoto arewa maso yammacin Najeriya sun bi sahun ƙasashen duniya wajen tunawa da wannan rana.

Taken ranar ta wannan shekara itace “shekaru 20 da fara irin wannan fadakarwar – An samu cigaba, amma da sauran aiki.

A yi wani abu domin kawar da matsalar kafin 2030” (“20 years on – progress but not enough! Act now to end fistula by 2030!”).

Matsalar yoyon fitsari matsala ce ta kiwon lafiya da yafi aukuwa lokacin haihu, kuma ya fi shafar mata a kasashen da basu cigaba ba mafi yawan lokutta sakamakon doguwar nakuda ba tare da an je asibiti ba. Kuma kashi 90 cikin 100 akan yi barin cikin in dai har mace ta samu yoyon fitsari.

Yoyon fitsari na faruwa ne sakamakon kafa (wata kofa) da ke samuwa tsakanin hanyar da jariri ke biyowa da ma’ajiyar fitsari ko kuma tsakanin hanyar da jariri ke biyowa da hanyar da bayan gida ke biyowa. Abinda ya sa ake kiran shi yoyon fitsari shine mafi yawan lokutta an fi samun hujewar ta wajen mafitsara fiye da ta hanyar da bayan gida ke biyowa.

A kashi na uku kuma ana samun wadanda duka biyun ya hade masu – watau hadewar hanyar da jariri ke biyowa da mafitsara, da ta hanyar da bayan gida ke biyowa. Sakamakon hakan masu matsalar na samun kan su cikin matsalolin kiwon lafiya saboda zama cikin kazanta , da rashin haihuwa, da ciwon damuwa sakamakon guje masu da ake yi da kuma tsunduma cikin talauci saboda barin sana’oin su da ya zama dole gare su saboda kyama da tsangwama da ake nuna masu, har ma da rasa ran mahaifiya da abinda ke cikin ta.

Yoyon fitsari dai abinda ya fi kawo shi shine tsawaitar nakuda ba tare da an haihu ba. Wannan na faruwa ne a saboda dalilai daban daban amma doguwar nakuda a gida ba tare da an je asibiti ba, ta fi samar da matsalar. Abinda ke faruwa shine a yayin da mace ta fara nakuda, kan jariri ke fara biyowa kafin gangar jiki.

To kan jaririn ne ke daukar lokaci yana gugar mafitsara (ma’ajiyar fitsari), ko kuma ya dade yana gugar hanyar da bayan gida ke biyowa, hakan ke kawo hujewar, wanda ke sa fitsari ko bayan gida ya canza hanyar da ya saba bi zuwa ga ta inda jariri ke biyowa. Kar mu manta ubangiji ya yi halittar dan adam yadda mutum zai iya rike fitsari ko bayan gida sai sun taru kuma ya ji lallai yana bukatar kewayawa sannan ya zagaya bayan gida ya fidda su.

To canza hanyar fitar bayan gidan ko fitsarin ke sa basu zuwa inda zasu taru sai muyum ya shirya fidda su, sai dai da sun zo sai su wuce su fita ta hanyar da jariri ke biyowa.

Labari mai dadi shine yoyon fitsari matsalace mai saukin kauce ma wa idan aka bi wadannan hanyoyi. Na farko itace zuwa asibiti idan mace na da ciki domin duba lafiyar ta da na jaririn da ta ke dauke da shi sannan a ba ta shawarwarin da zasu taimaka wajen kare lafiyar ta da na abinda ta ke dauke da shi. Na biyu kuma lokacin da ta fara nakuda.

Wannan zai sa a dauki matakin kariya idan an hango wata matsala wajen haihuwar, irin matsalolin da ba za’a iya hangowa ba idan aka tsaya a gida.

Idan kuma mace ta samu matsalar yoyon fitsarin, akwai cibiyoyin da gwamnatin tarayya da jihohi suka kafa musamman don magance matsalar kyauta tare da gudunmuwar kungiyoyin masu zaman kan su da tallafin majalisar dinkin duniya da gwamnatocin Amurka da Canada da sauran su wadanda ke hadaka da gwamnati domin biyan kudin aikin kasancewar yawancin matsalar tana shafar mata ne da basu da galihu.

Akwai dalilan da ke hana mata zuwa cibiyoyin lafiya sun hada da rashin sanin illar haihuwa a gida saboda al’ada da jahilci, da rashin kudin motar zuwa cibiyar haihuwa saboda talauci da nisa da yanayin rashin kyaun hanya, da rashin ma’aikaciyar jiyya mace a wasu cibiyoyin wanda ke sa mata ba su son ma’aikacin jiyya namiji ya karbi haihuwar su. Amma kuma zai fi dacewa ma’aikacin jinya namiji ya karbi haihuwar, da a ce shi namijin ne zai yi ma mace aiki idan ta samu matsalar yoyon fitsari.

Daga karshe don magance matsalar, ana bukatar wayar da kan jama’a musamman na karkara domin zuwa cibiyoyin kiwon lafiya idan an fara nakuda.

Sannan yana da muhimmanci kwarai a magance dalilan da ke hana zuwa haihuwar a cibiyoyin da gwamnati ta amince da su ta hanyar samar da motocin daukar mara lafiya a kauyuka da ke nesa da cibiyar kiwon lafiya.

Comments are closed.