Take a fresh look at your lifestyle.

Gwamna Mbah Ya Bada Umurnin Dakatar da Asusun Gwamnatin Jihar Enugu

0 91

Gwamna Peter Mbah na jihar Enugu ya ba da umarnin a kulle duk wani asusun ajiyar banki na gwamnati nan take har sai an sanar da shi.

 

An bayyana hakan ne ta wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Chidiebere Onyia, ranar Talata a Enugu.

 

A cewar Onyia, umarnin zai fara aiki daga ranar 30 ga Mayu.

 

“Bisa umarnin da gwamnan jihar Enugu ya bayar na rufe dukkan asusun gwamnati a dukkan bankunan jihar Enugu, na ba da umarnin a kulle dukkan asusun gwamnatin jihar Enugu ba tare da bata lokaci ba, har sai an samu sanarwa,” in ji Onyia.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *