Take a fresh look at your lifestyle.

Shugaba Tinubu Ya Gana Da Shugabannin Tsaro

0 215

A halin yanzu dai shugaba Bola Tinubu yana ganawa da hafsoshin tsaron Najeriya karkashin jagorancin Babban Hafsan Sojin Kasa Janar Lucky Irabor a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Shugaban hafsan tsaron ya jagoranci hafsoshin tsaro da sauran shugabannin hukumomin tsaro da misalin karfe 10:30 agogon GMT domin taron tsaro.

Wadanda suka halarci taron sun hada da babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Farouk Yahaya; Babban Hafsan Sojin Ruwa, Vice Admiral Awwal Gambo; Shugaban hafsan sojin sama Air Marshal Isiaka Amao da Sufeto-Janar na ‘yan sanda Usman Alkali Baba.

Sauran sune Darakta-Janar na Hukumar Tsaro ta farin kaya (DSS), Yusuf Bichi; Darakta-Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA), Ahmed Rufa’i Abubakar.

Taron da ke gudana dai shi ne ganawa ta farko da shugaba Tinubu ya yi da shugabannin hukumomin tsaro da na leken asiri na kasar tun bayan hawansa mulki a ranar Litinin, 29 ga watan Mayu.

Shugaban ya gana da Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC), Abdulrasheed Bawa a fadar Villa ranar Laraba.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *