Shugaba Bola Tinubu na ganawa da shugabannin majalisar dokokin kasar a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Wadanda suka halarci taron sun hada da shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan, kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila da sauran manyan jami’an majalisar.
Muryar Najeriya ta rawaito cewa har yanzu ba a bayyana dalilin taron ba amma mai yiwuwa; yana da nasaba da batun fitowar shugabannin majalisar ta 10 da za a kaddamar a karshen wannan watan.
Tun da farko dai shugaban kasar ya gana da jami’an tsaro, inda suka yi masa bayani kan matsalar tsaro a kasar.
Cikakken bayani anjima…
Leave a Reply